Home Labaru Ilimi Ilimi: Yara Miliyan 19 A Najeriya Ba Sa Zuwa Makaranta-Adamu...

Ilimi: Yara Miliyan 19 A Najeriya Ba Sa Zuwa Makaranta-Adamu Adamu

361
0

Tsohon ministan ilimi a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari zangon farko, Adamu Adamu, ya bayyana cewa adadin yara da ba sa zuwa makaranta a Najeriya sun haura miliyan 19.

Adamu,  ya kasance daya daga zababbun mutane 43 da shugaban kasa Buhari ya sake aikewa da sunayen su zuwa majalisar dattawa domin tantancewa a matsayin minista a sabuwar gwamnatinsa.

Tsohon ministan ilimi a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari

Tsohon ministan ya ce a sabuwar kididdigar alkalumma gami da kidaya da aka fitar cikin watan Fabrairun 2019 ta bayyana cewa, akwai fiye da yara miliyan 19 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya .

Adamu, ya ce adadin yaran da ba sa zuwa makarantun firamare sun kai kimanin miliyan goma, yayin da miliyan 9 marasa zuwa makarantun sakandire ke ci gaba da gararamba a Najeriya.

Adamu ya bayyana hakan ne a lokacin da majalisaa dattawa ke yi masa tamboyoyi a zauren majalisa, ya alakanta mummunan lamari da gazawar gwamnatin tarayya da kuma ta jihohi wajen karkatar da akalar muhimmanci zuwa ga ingancin ilimi.

Tsohon ministan ya ce har yanzu akwai miyagun mutane da dama a Najeriya wadanda  suka yi kane-kane wajen aikata laifuka na rashawa da kuma barazana ga tattalin arziki duk da akidar yaki da cin hanci da rashawa ta gwamnatin Buhari.