Gwamnatin jihar Kano ta ce, ba za ta taba sauka daga matsayinta ba kan dokar sabbin masarautun da ta kirkiro guda hudu.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya mika sandar Girma ga sabbin sarakunan duk da umarnin da wata kotu ta bayar na dakatar da taron bikin.
Mai martaba Sarkin Kano Muhammad Sunusi Sunusi, ya isa filin jirgin saman na Malam Aminu Kano a yammacin jiya Lahadi bayan ya dawo daga aikin Umra a kasar Saudiya, inda masoyansa suka yi masa tarba ta musamman cikin farin ciki, yayinda suka yi masa rakiya zuwa fadar sa.
Da dama daga cikin magoya bayansa suka yi ado da riguna da huluna dauke da sunan basaraken, yayin da wasu kuma suke kade-kade da raye-rayen maraba.
Rahotanni na cewa, Sarkin bai yi wani jawabi ba bayan isowarsa Najeriya daga Saudiya.
Sign in
Welcome! Log into your account
Forgot your password? Get help
Password recovery
Recover your password
A password will be e-mailed to you.