Home Labaru Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutane 2 A Jihar Niger

Garkuwa Da Mutane: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutane 2 A Jihar Niger

281
0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a karkashin shirin Operation Puff Adder ta sami nasarar cafke masu garkuwa da mutane uku a jihra niger.
Kakakin rundunar yan sandan Najeriya, Frank Mba ne ya bayyana haka a Abuja, ya ce sun kwato bindigogi guda biyu kirar AK 47 da alburusai da dama.
Mba, ya bayyana sunayen mutanen da suka kubutar sun hada Ali Abu Sale mai shekaru 34 da Bala Bawa mai shekaru 37, wadanda ‘yan bindigar suka sace daga kauyen Maijaki dake karamar hukumar Lapai na jahar Neja.
Mba, ya kara da cewar sun ceto Sale ne daga dajin Mai Lamba dake kusa da garin Lapai, ya yin da suka ceto Bawa a kauyen Gada Biyu dake wajen Abuja.
Haka zalika ya bayyana sunayen masu garkuwa da mutanen da suka da Mohammed Bello da ake yi wa inkiya da ‘Dan Hajiya mai shekaru 42, da Suleiman Musa mai inkiya da ‘Dan Auta mai shekaru 38, da kuma Abubakar Bello mai inkiya da Abu Kango mai shekaru 28, sai kuma wani guda daya da ya mutu a msayar wuta da ‘yan sanda.