Kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, sun caccaki Shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole a kan rikirkita al’amurran jam’iyyar.
A cikin wata wasika da su ka aike wa Oshiole, Babban Daraktan kungiyar Salihu Lukman, ya ce abubuwa sun kara tabarbarewa a jam’iyyar APC.
Lukman, ya ce ya fahimci babu wani bambanci tsakanin yadda Oshiomhole ke tafiyar da jam’iyyar da kuma yadda John Oyegun ya tafiyar da ita a lokacin shugabancin sa.
Ya ce maimakon a samu ci-gaba, abubuwa sun kara tabarbarewa, kuma matsalolin shugabanci da jam’iyyar ke fuskanta su na kara zurfafa a halin da ake ciki.
Kungiyar, ta alakanta faduwar da su ka yi a zaben gwamna a jihohin Zamfara da Oyo da Imo da Bauchi da Adamawa a kan rikcin cikin gida, wanda Adams Oshiomole ya haddasa, ta na mai gargadin cewa hakan na iya kasancewa a jihohin Kogi da Ondo da Edo.
A karshe ya bukaci Oshiomole ya bada damar tattaunawa domin lalubo hanyoyin magance matsalolin da su ka yi wa jam’iyyar APC dabibayi.