Home Labaru Tsaro: Hukumar Tsaro Ta Civil Deffence Ta Fara Daukar Sabbin Ma’aikata

Tsaro: Hukumar Tsaro Ta Civil Deffence Ta Fara Daukar Sabbin Ma’aikata

2293
0

Ma’aikatar cikin gida ta Nijeriya na sanar da musamman matasa cewa, ta fara karbar takardun masu sha’awar aiki a hukumar tsaro ta farin kaya Civil Defence.

Rukunin farko da mutanen da hukumar ke nema sun hada da Likitocin hakora, da na ido, wadanda ta ke bukatar su nuna shaidar kammala karatun digiri da shaidar lasisin fara aiki daga wajen su.

Haka kuma, rukuni na biyu ana bukatar jami’ai masu mukamin Sufeta, da wadanda su ka yi karatun jinya da kuma ungozoma, inda ta ke neman su kasance su na da rajista da cibiyar ungozoma ta Nijeriya.

Sai kuma matakin mataimakin Sufeto na daya, wanda hukumar ke neman mutanen da ke da takardar Difloma a ilimin kiwon lafiya, da tattara bayanan marasa lafiya da kimiyyar hada magani da abinci mai gina jiki da direbobi da sauran su.

Ana bukatar duk masu son shiga aikin su bi ta adireshin hukumar na yanar gizo, inda za su cike bayanan su tare da sauke takardun da masu tsaya masu za su cika, kuma za kammala a cikin makonni 4, wato daga ranar 10 ga watan Agusta zuwa 7 ga watan Satumba na shekara ta 2019.

Leave a Reply