Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Gwamnonin APC Sun Dora Alhaki Rikirkita Al’amurran Jam’iyyar A Kan Adams Oshiomole

Oshiomhole Ya Jinjinawa Buhari Bisa Rage Kudin Man Fetur

Adams Oshiomhole, Shugaban Jam’iyyar APC Ta Kasa

Kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, sun caccaki Shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole a kan rikirkita al’amurran jam’iyyar.

A cikin wata wasika da su ka aike wa Oshiole, Babban Daraktan kungiyar Salihu Lukman, ya ce abubuwa sun kara tabarbarewa a jam’iyyar APC.

Babban Daraktan kungiyar Salihu Lukman

Lukman, ya ce ya fahimci babu wani bambanci tsakanin yadda Oshiomhole ke tafiyar da jam’iyyar da kuma yadda John Oyegun ya tafiyar da ita a lokacin shugabancin sa.

Ya ce maimakon a samu ci-gaba, abubuwa sun kara tabarbarewa, kuma matsalolin shugabanci da jam’iyyar ke fuskanta su na kara zurfafa a halin da ake ciki.

Kungiyar, ta alakanta faduwar da su ka yi a zaben gwamna a jihohin Zamfara da Oyo da  Imo da Bauchi da Adamawa a kan rikcin cikin gida, wanda Adams Oshiomole ya haddasa, ta na mai gargadin cewa hakan na iya kasancewa a jihohin Kogi da Ondo da Edo.

A karshe ya bukaci Oshiomole ya bada damar tattaunawa domin lalubo hanyoyin magance matsalolin da su ka yi wa jam’iyyar APC dabibayi.

Exit mobile version