Jam’iyyar African Action Alliance AAC, ta kori shugaban ta na kasa Omoyele Sowore, bayan kotu ta bada umarnin ci-gaba da tsare shi har tsawon kwanaki 45 kafin a kammala bincike game da zanga-zangar juyin-juya-halin da ya kitsa.
Haka kuma, Jam’iyyar ta sallami wasu karin ‘ya’yan ta 28, yayin da ta maye gurbin Sowore da Dr. Leonard Nzenwa a matsayin shugaban ta na kasa.
Wannan dai ya na zuwa ne, bayan mai shari’a Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya ya ba Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS umarnin ci-gaba da tsare Sowore bisa zargin aikata laifin ta’addanci.
Wasu hujjoji da Hukumar DSS ta gabatar wa kotu, sun hada da hoton bidiyon da ke nuna Sowore ya na ganawa da Nnamdi Kanu, yayin da wani hoton bidiyo ya nuna wasu kalaman sa da ke cewa za su hada hannu da haramtacciyar Kungiyar ‘yan Shi’a domin gurgunta gwamnatin Nijeriya.
Hukumar DSS, ta ce an kama Sowore ne saboda shirya zanga-zangar juyin-juya-halin da ya kira a duk fadin Nijeriya da zummar nuna rashin amincewa da salon mulkin Nijeriya.