Home Labaru Kiwon Lafiya Riga-Kafi: Nijeriya Ta Na Shirye-Shiryen Tunkarar Cutar Coronavirus

Riga-Kafi: Nijeriya Ta Na Shirye-Shiryen Tunkarar Cutar Coronavirus

412
0
Riga-Kafi: Nijeriya Ta Na Shirye-Shiryen Tunkarar Cutar Coronavirus
Riga-Kafi: Nijeriya Ta Na Shirye-Shiryen Tunkarar Cutar Coronavirus

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Nijeriya, ta fara shiryen-shirye a kan yadda za ta tunkari cutar coronavirus idan ta bulla a kasar nan.

A cikin wani sako da ta wallafa a shafin ta na Twitter, hukumar ta ce tawagar da ke shirye-shirye a kan cutar bisa tallafin hukumar lafiya ta duniya a Nijeriya, ta na karbar bakuncin wani taron yini biyu domin tunkarar cutar.

An dai tsara gudanar da taron ne domin karfafa matakan kariya idan aka samu bullar cutar a Nijeriya.