Hukumar hana yaduwar cututtuka ta Nijeriya, ta fara shiryen-shirye a kan yadda za ta tunkari cutar coronavirus idan ta bulla a kasar nan.
A cikin wani sako da ta wallafa a shafin ta na Twitter, hukumar ta ce tawagar da ke shirye-shirye a kan cutar bisa tallafin hukumar lafiya ta duniya a Nijeriya, ta na karbar bakuncin wani taron yini biyu domin tunkarar cutar.
An
dai tsara gudanar da taron ne domin karfafa matakan kariya idan aka samu bullar
cutar a Nijeriya.

