Home Labaru Difilomasiyya: Nijar Ta Mika Wa Nijeriya Tubabbun Mayakan Boko Haram 25

Difilomasiyya: Nijar Ta Mika Wa Nijeriya Tubabbun Mayakan Boko Haram 25

302
0
Difilomasiyya: Nijar Ta Mika Wa Nijeriya Tubabbun Mayakan Boko Haram 25
Difilomasiyya: Nijar Ta Mika Wa Nijeriya Tubabbun Mayakan Boko Haram 25

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ta mika wa Nijeriya tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram 25 da su ka ajiye makaman su.

Tuni dai aka yi jigilar mutanen 25 zuwa Maiduguri, a karkashin jagorancin babban jami’in da ke kula da shirin horar da irin wadannan mutane Janar Bamidele Ashafa.

Janar Ashafa ya ce, za su mika mutanen 25 ga gwamnatin Jihar Barno domin kula da su.

Ya ce za su cigaba da karfafa wa irin wadannan mutane gwiwa don ganin sun ajiye makaman su da nufin rungumar shirin gwamnatin Nijeriya na zaman lafiya.

Kwamishiniyar kula da harakokin mata ta Jihar Barno da ta karbe tubabbun, tace za su ciyar da su da tufatar da su da kuma sake tunanin su tare da koya masu sana’oi a cibiyar da gwamnan jihar Farfesa Babagana Zulum ya samar.