Home Labarai Rashin Tsaro: Za A Yi Zaben 2023, Shugaban Tsaro Ya Tabbatarwa Yan...

Rashin Tsaro: Za A Yi Zaben 2023, Shugaban Tsaro Ya Tabbatarwa Yan Najeriya

70
0

Babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Lucky Irabor, ya ba ‘yan Nijeriya tabbacin cewa za a gudanar da zaben shekara ta 2023.

Da ya ke jawabi a wani taron manema labarai a helkwatar tsaro ta kasa da ke Abuja, Janar Irabor ya ce sojoji za su yi duk mai yiwuwa domin ganin babu abin zai hana gudanar da zaben.

Janar Irabor, ya kuma nanata kudurin sojin Nijeriya na kare manufofin dimokaradiyya a kasar da ta fi yawan al’umma a yankin Afirka, inda ya ce sojoji sun yi alkawarin kare dimokuradiyyar Nijeriya kuma ba za su canza daga matsayin su ba.

An dai gudanar da taron ne don neman goyon bayan kafofin yada labarai domin tunkarar kalubalen tsaro a Nijeriya.

Wannan dai shi ne karo na biyu a jerin tattaunawa tsakanin babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya da shugabannin zartarwa da editocin kafofin yada labarai na Nijeriya.