Home Labarai An Kori Wani Ɗan Sanda Da Ya Ci Zalin Wani Mutum A...

An Kori Wani Ɗan Sanda Da Ya Ci Zalin Wani Mutum A Nijeriya

127
0

Hukumar ‘yan sandan Nijeriya, ta kori daya daga cikin ma’aikatan ta saboda cin zarafin wani farar hula.

Jami’in mai suna Liyomo Okai da ke aiki a babban ofishin ‘yan sanda na Ekori a Jihar Rivers, an gan shi ne a wani bidiyo ya na dukan wani mutum da adda.

Rundunar ‘yan sandan ta sanar da haka ne a shafin ta na Tuwita, inda ta ce korar jami’in ta fara aiki nan take daga ranar 8 ga watan Agusta.

Shugaban ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba, ya bayyana matukar takaicin sa a kan rahoton cin zarafin da ƙwace da ake tuhumar wasu ‘yan sanda a ƙorafe-ƙorafen da jama’a su ka gabatar a kafafe daban-daban da aka gabatar.

Usman Alkali Baba, ya kuma ba duk kwamishinonin hukumar umarnin tabbatar da sa ido sosai da kula da ayyukan jami’an ta a kan faruwar irin waɗannan abubuwa.

Leave a Reply