Home Labarai PDP Ta Dage Taron Ta Na NEC Da Majalissar Wakilai

PDP Ta Dage Taron Ta Na NEC Da Majalissar Wakilai

55
0

Jam’iyyar PDP, ta dage taron ta na kwamitin zartarwa na kasa da ‘yan majalisar wakilai, biyo bayan dambarwar da ta dade tsakanin dan takarar ta na shugaban kasa Atiku Abubakar da gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers da ke kara dagulewa.

Tun farko dai an shirya gudanar da tarurruka biyu masu muhimmanci ne a ranakun Laraba da kuma Alhamis.

A cikin Wata sanarwa da sakataren jam’iyyar PDP na kasa Sanata Samuel Anyanwu ya fitar, ta ce an dage zaman ne saboda wasu abubuwan da su ka bullo da ba a yi tsammani ba.

Duk da cewa sakataren bai bayyana dalilin da ya sa aka dage taron ba, majiyoyi sun ce sun yanke shawarar hakan ne sakamakon matsaya mai tsauri da gwamna Wike ya dauka a yunkurin sulhun su da Atiku.

Daga cikin wasu bukatu da dama, bangaren Wike ya yi kira ga shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu da ya sauka daga mukamin sa, ya bar daya daga cikin mataimakan sa daga yankin Kuduncin Nijeriya ya maye gurbin sa.