A jamhuriyar Nijar, a yankin Tillabéri, yara 53,562 ne ba sa zuwa makarantata dalilin rashin tsaro duk da kasancewar jami’an tsaro na (FDS) da kuma sintirin da suke yi a yankini.
A Torodi kaɗai rahotani sun ambato cewa sama da makarantu 100 ne aka rufe a dalilin matsalar rashin tsaron.
Yankunan kan iyaka da Nijar da Burkina Faso ne suka fi fama da wannan matsalar, yankunan da ke ci gaba da fuskantar barazanar hare-hare daga ƙungiyoyin masu kai hare-hare.
Sai dai kuma dakarun tsaron ƙasar na ƙoƙari wajen ganin kwanciyar hankali da zaman lafiya sun dawo da za su bada damar cigaba da karatu a yankunan.