Golan Manchester City Stefan Ortega ya samu gayyatar farko a tawagar Jamus bayan da koci Julian Nagelsmann ya sanya sunan sa cikin wadanda suka wakilci ƙasar a Nations League a ranar Alhamis.
Ɗan wasan mai shekaru 32 zai haɗu da Alexander Nübel na Stuttgart da Oliver Baumann na Hoffenheim a matsayin daya daga cikin masu tsaron gida uku cikin tawagar ƴan wasa 23 na Jamus.
Mai tsaron gidan Jamus mai lamba ɗaya, Marc-André ter Stegen na Barcelona, na ci gaba da jinya saboda mummunan rauni da ya samu a gwiwa.
Ƴan wasan tsakiya na Borussia Dortmund Julian Brandt da Felix Nmecha suma an sake kiran su cikin tawagar ta Jamus.