Shugaban ƙasar Iran Masoud Pazeshkian ya ce ƙasar ba ta damu da ko wanene ya lashe zaɓen shugaban ƙasa da aka kammala a Amurka ba.
Sai dai kuma gwamnatin Iran ɗin ta kira nasarar Donald Trump da wata dama ga Amurka ta nazarin abin da ta kira manufofin ta marasa kyau na baya, domin ta gyara.
Donald Trump dai ya dauki matakai tsaurara kan kasar ta Iran lokacin wa’adin mulkin sa na farko.