Home Coronavirus Ramadan: Yadda Sheikh Dahiru Bauchi Zai Yi Tafsiri

Ramadan: Yadda Sheikh Dahiru Bauchi Zai Yi Tafsiri

1190
0

Shahararren malamin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya sanar da yadda tsarin Tafsirinsa na wannan shekarar zai kasance.

Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya saba gudanar da Tafsirin wata Ramadan a Kaduna ya ce zai gabatar da Tafsirin bana ne ta yadda ba sai mutane sun halarci majalisin karatun ba.

A ganawarsa da ‘yan jarida a ranar Laraba, shehin malamin ya ce zai gabatar da tafsirin wannan shekarar ne a jihar Bauchi, ba sai jama’a sun taru domin halartar majalisin da ya saba yi a Kaduna ba.

Ya ce ‘yan jarida daga Kaduna da takwarorinsu daga sauran wurare za su dauki Tafsirin, sanan a watsa a duniya ta kafafen yada labarai.

Kawo yanzu dai babu tabbaci game da yiwuwar barin dubun dubatar almajiran malamin su halarci majalisin Tafsirin da zai gabatar a jihar Bauchi.

A halin yanzu an sanya dokar hana zirga-zarga tare da rufe iyakokin jihohin jihar Kaduna da sauran makwabtanta a wani mataki na kokarin dakile yaduwar cutar coronavirus.

Jihohin Kaduna da Bauchi na daga cikin jihohin da aka samu bullar annobar wadda ta kama gwamnonin jihohin biyu.

Gwamnan Bauchi Bala Muhammad ya warke, amma har yanzu babu labarin warkewan takwaransa na Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa’i.

Ya zuwa yanzu annobar COVID-19 ta yi ajalin mutum 11 a Najeriya, inda sama da mutum 270 suka harbu ita.