Home Coronavirus Buhari Ya Gana Da Kwamitin Yaki Da Coronavirus

Buhari Ya Gana Da Kwamitin Yaki Da Coronavirus

286
0
Gwamnatin ba ta bayyana abin taron ya tattauna ba.

Shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da Kwamitin Aiki Da Cikawa Na Fadar Shugaban Kasa Kan Yaki Da Cutar Coronavirus daga nesa.

Buhari ya gana da jami’an kwamitin ne ta fasahar video conference call, wadda amfani da ita ke karuwa domin gujewa yaduwar cutar.

Fadar Shugaban Kasa ta fitar da hoton Shugaba Buhari zaune a fadar gwamnati a lokacin taron na ranar Laraba.

Sai dai gwamnatin ba ta bayyana abin taron ya tattauna a kai ba, amma ana kyautata zaton kwamitin ya yi wa shugaban kasar bayani game da aikinsa.