Home Coronavirus Coronavirus Ta Yi Kisa A Kano

Coronavirus Ta Yi Kisa A Kano

651
0
Kwana 5 da bullar cutar coronavirus a jihar Kano har yawan masu ita a ya haura mutum 20.
Kwana 5 da bullar cutar coronavirus a jihar Kano har yawan masu ita a ya haura mutum 20.

Cutar coronavirus ta kashe mutum na farko a jihar Kano, yayin da yawan masu dauke da ita ya karu zuwa mutum 21 a jihar.

Ma’aikatar Lafiyar Jihar Kano ta sanar da mutuwar mutumin da cutar ta fara kashewa a jihar ne a ranar Laraba.

Ma’aikatar ta kuma sanar da karuwar mutum 12 da suka harbu da cutar, da misalin karfe 11:55 na dare, lamarin da ya yi sanadiyar karuwar masu cutar COVID-19 a jihar zuwa mutum 21.

Mamacin ya shigo jihar Kano ne daga Abuja kafin gwamnatin jihar ta rufe hanyoyinta ga masu shigowa daga wasu jihohi da nufin hana yaduwar annobar, a cewar hukumomin.

Mutuwar da kuma tashin gwauron zabi na masu cutar COVID-19 a jihar Kano na zuwa ne a jajibirin ranar da hukumomi za su fara aiwatar da dokar hana fita na mako guda domin dakile yaduwar annobar a fadin jihar.

Dokar hana fitar ta haramta budewa shaguna da kasuwanni da dukkanin nau’ikan taron jama’a.

A ranar Asabar ne hukumomin jihar suka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar a jihar, amma cikin kwana biyar har yawan masu cutar a jihar ya haura 20.