Home Coronavirus PDP, El-Rufa’i Ya Tsawaita Rufe Kaduna Na Tsawon Kwanaki 30

PDP, El-Rufa’i Ya Tsawaita Rufe Kaduna Na Tsawon Kwanaki 30

343
0
PDP, El-Rufa’i Ya Tsawaita Rufe Kaduna Na Tsawon Kwanaki 30
PDP, El-Rufa’i Ya Tsawaita Rufe Kaduna Na Tsawon Kwanaki 30

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kaduna, ta soki lamirin Gwamna Nasir El-Rufai a kan tsawaita dokar hana fita da ya yi zuwa tsawon wasu kwanaki 30.

PDP ta yi zargin cewa, abin da ya fi damun gwamnatin jihar Kaduna kawai su ne, kudaden shigar da za ta samu daga tarar da ta ci wadanda su ka saba dokar.

Yayin da ta ke sukar tsarin yadda gwamnatin jihar ke bi wajen hana yaduwar COVID-19, PDP ta ce gwamnatin APC ba ta yi wa al’umma karin haske game da irin nasarar da ake samu ba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP a jihar Kaduna Abraham Catoh, ya ce rufe jihar Kaduna da aka yi wani salo ne na samun kudi ba wai kawo karshen Coronavirus ba.

Sai dai shugaban jam’iyyar APC na jihar Kaduna Emmanuel Jekada, ya bayyana zargin PDP a matsayin maras amfani, ya na mai cewa rufe jihar da aka yi domin amfanin al’umma ne da ba ya bukatar a siyasantar da shi.