Home Labaru P & ID: Gwamnatin Tarayya Ta Na Binciken Asusun Jonathan Da Diezani

P & ID: Gwamnatin Tarayya Ta Na Binciken Asusun Jonathan Da Diezani

534
0
P & ID: Gwamnatin Tarayya Ta Na Binciken Asusun Jonathan Da Diezani
P & ID: Gwamnatin Tarayya Ta Na Binciken Asusun Jonathan Da Diezani

Gwamnatin tarayya ta bukaci a ba ta bayanan kudin da ke shiga asusun wasu tsofaffin shugabanni da jami’an da su ka rike mukamai a lokacin mulkin jam’iyyar PDP.

Daga cikin wadanda ake tunanin gwamnati na son samun rahoto game da asusun bankin su har da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da mai dakin sa Patience Jonathan.

Sauran wadanda ake bincike a kan su sun hada da tsofaffin ministocin man fetur Diezani Alison-Madueke da marigayi Rilwanu Lukman.

Bankunan da ake bibiya kuwa sun hada Citigroup, da JPMorgan Chase da kuma Deutsche Bank AG, sakamakon  binciken wata kwangilar gas da Nijeriya ta yi da kamfanin P&ID da Gwamnatin tarayya ke yi.

Hukumar EFCC ce ta ke gudanar da bincike domin ta gano wadanda ke da hannu a badakalar da aka tafka a wannan kwangila ta P&ID da sunan za a kafa wani kamfanin gas a Nijeriya.