Home Labaru Polaris Bank Ya Fitar Da Sakamakon Kididdigar Kudaden Sa

Polaris Bank Ya Fitar Da Sakamakon Kididdigar Kudaden Sa

345
0
Polaris Bank Ya Fitar Da Sakamakon Kididdigar Kudaden Sa
Polaris Bank Ya Fitar Da Sakamakon Kididdigar Kudaden Sa

Bankin Polaris, ya fitar da sakamakon kididdigar kasa da kasa ta hada-hadar kudaden sa na  shekara ta 2019. 

Bankin ya bayyana naira biliyan 27 da miliyan 800 a matsayin ribar da ya samu, yayin da ya bayyana mallakar naira biliyan 150 da miliya 800 a shekara ta 2019.

Haka kuma, bankin ya ce ya zuwa karshen shekara ta 2019, ya mallaki kadarorin da kiyasin su ya kai naira Tiriliyan 1 da biliyan 100, da kuma kudaden hannun jari da yawan su ya kai naira biliyan 83.

Shugaban Bankin kuma babban jami’in gudanarwa na bankin  Mr. Adetokunbo Abiru, yay aba da irin gudunmuwar da manyan daraktocin Bankin da Babban Bankin Nijeriya CBN su ka bada domin cimma nasarorin da bankin ya samu.

Tuni dai kididdiga ta tabbatar da cewa, Bankin Polaris ya cika duk wasu sharuddan da ake bukata a fagen hada-hadar kudade ta Nijeriya.