Karamin ministan ilmi Emeka Nwajiuba, ya ce har yanzu bai ga ranar da za a bude makarantu domin ci-gaba da karatun dalibai a fadin Nijeriya ba.
Emeka Nwajiuba ya bayyana haka ne, yayin da ya ke amsa tambayoyi a wajen taron manema labarai da kwamitin shugaban kasa da ke yaki da cutar COVID-19 ta shirya a Abuja.
Ya ce duk da gwamnatin tarayya ta sassauta takunkumin kulle babu ranar sake bude makarantu tukuna.
Karamin ministan ya kara da cewa, shugaban kasa ya fara tabo batun bude tattalin arziki sannu a hankali, kuma idan har ba a yi wannan ba, ba ya ganin akwai lokacin da za a sake bude makarantu.
Ya ce muddin shugaban kasa bai fara maganar jama’a su koma wuraren aikin su ba, to ba zai iya cewa ga ainihin lokacin da za a sake bude makarantun da ke fadin kasar nan ba.














































