Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta kasa a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.
Zaman dai, ya kasance na biyu da Osinbajo ke jagoranta tun bayan da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Nijeriya a ranar 28 ga watan Oktoba.
Da farko dai shugaba Buhari ya halarci wani taro ne a kasar Saudiyya, yanzu haka kuma ya na ziyarar sa-kai a birnin Landan.
Rahotanni
sun ce ana sanya ran dawowar shugaba Muhammadu Buhari Nijeriya ranar 17 ga
watan Nuwamba na shekara ta 2019.














































