Home Labaru Ba Datse Iyakokin Nijeriya Ne Mafita Ba – Okorocha

Ba Datse Iyakokin Nijeriya Ne Mafita Ba – Okorocha

331
0
Rochas Okorocha, Tsohon Gwamnan Jihar Imo
Rochas Okorocha, Tsohon Gwamnan Jihar Imo

Tsohon gwamnan jihar Imo sanata Rochas Okorocha, ya ce ba rufe iyakokin Nijeriya ne mafita ba idan har ana so a bunkasa tattalin arzikin kasa da sama wa matasa aikin yi.

Ya ce akwai sama da iyakoki 3000 da ke zagaye da Nijeriya, tun daga kasashen Benin, a Kamaru, da Nijar, da Togo, da Ghana, da Chadi, kuma dajin Allah da za iya shigo Nijeriya ta ko ina.

Okorocha ya kara da cewa, duk da ya na goyon bayan maida hankalin da aka yi wajen ganin an bunkasa noman abinci a cikin gida Najeriya, hakan ba shi ne zai sa kubuta daga mastsalar da ake fama da ita ba.

Ya ce sai an sama wa matasa ayyukan yi ta hanyar kafa masana’antun da za su samu aiki.