Home Labaru Martani: Babu Rashin Jituwa Tsakanin Buhari Da Osinbajo – FGN

Martani: Babu Rashin Jituwa Tsakanin Buhari Da Osinbajo – FGN

275
0

Fadar Shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin da ke cewa akwai rashin jituwa tsakanin ofishin Shugaban kasa da na mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo.

Mai ba Shugaban kasa shawara ta musamman a kan harkokin majalisar dokoki ta tarayya Sanata Babajide Omowurare ya bayyana haka, yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi a majalisar dokoki ta kasa da ke Abuja.

Da ya ke maida martani ga masu sukar hukuncin shugaba Buhari na sa hannu a wata doka a birnin London, Sanata Omowrare ya ce lallai kundin tsarin mulki ya ba Shugaban kasa damar aiki daga ko ina.

Ya ce lamarin ya sha bamban da na tsoho Shugabannin kasa Umaru ‘Yar’adua da mataimakin sa Goodluckk Jonathan, inda ta kai a lokacin da tsohon Shugaban kasar ba ya iya aiwatar da ayyukan sa saboda tsananin rashin lafiya.

Sai dai kuma ya yi gum da bakin sa, a kan dalilin da yasa Shugaban Buhari bai aika wata wasika zuwa ga majalisar dokoki ta domin mika ragamar aiki ga mataimakin Shugaban kasa.