Home Labaru Oshiomhole Na Min Bita-Da-Kulli – Al-Mustapha Audu

Oshiomhole Na Min Bita-Da-Kulli – Al-Mustapha Audu

773
0

Dan tsohon gwamnan jihar Kogi Almustapha Audu, ya ce shugaban Jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ne da kan sa ya ke kulla ma shi makirci don kada a ba shi tikitin takarar kujerar gwamnan jihar Kogi a karkashin jam’iyyar APC.

Audu ya bayyana haka ne, yayin wata zantawa da ya yi da manema labarai, inda ya ce da gangan Oshiomhole yake shirya masa tuggu don kada jam’iyyar ta tsaida shi dan takarar ta.

Ya ce idan jam’iyyar APC ta na neman kudi su kan je wurin shi ya ba su ko nawa ne, amma yanzu da ya kai ga za su yi takara, kiri-kiri su na yi ma shi kumbiya-kumbiya har zun zare sunan sa cewa cancanci takara ba.

A wani martani da jam’iyyar APC ta maida wa Mustapha, ta ce ya mika mata wasu takardun sa da ba su yi daidai da gaskiyar bayani a kan sa ba, kuma takardar haihuwar sa ta nuna an haife shi a shekara ta 1959, amma a fasfon sa ya nuna shekara ta 1960.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/libertytvnews

Twitter: https://twitter.com/libertytvnews

Instagram: https://instagram.com/libertytvng

Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??

zeno.fm/libertyradioabuja

Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?

Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.

Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com

Leave a Reply