Home Labaru Yadda Aka Kwato Mataimakin Gwamna A Hannun ‘Yan Bindiga

Yadda Aka Kwato Mataimakin Gwamna A Hannun ‘Yan Bindiga

1726
0

Hukumar tsaro ta farar hula a jihar Nasarawa, ta yi nasarar kwato wasu mutane bakwai da barayi su ka yi garkuwa da su a makon da ya gabata, ciki har da mataimakin gwamnan jihar Dakta Emmanuel Akabe.

Kwamandan rundunar tsaro ta Civil Defence a jihar Nasarawa Muhammad Gidado Fari, ya ce ‘yan kundunbalar hukumar ne su ka ceto wadanda aka yi garkuwa da su, sai dai masu garkuwar sun arce da gudu kafin jami’an su su isa dajin.

Daya daga cikin wadanda aka ceto, ya ce sun sha azabar tafiya mai nisa cikin daji da rashin abinci, kuma sai da su ka biya kudin fansa.

A halin da ake ciki dai, rundunar ‘yan sanda ta jihar Nasarawa ta ce, ta kama mutane uku da ta ke zargi da fashi da makamin da ya yi sanadin mutuwar jami’an ta uku da ke tsaron lafiyar mataimakin gwamnan jihar da wasu mutane biyu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/libertytvnews

Twitter: https://twitter.com/libertytvnews

Instagram: https://instagram.com/libertytvng

Liberty Radio 103.3 FM Abuja Kai Tsaye A Yanar Gizo ??

zeno.fm/libertyradioabuja

Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna Kai Tsaye A Yanar Gizo ??
zeno.fm/tasharyancikaduna ?

Kira ??? +1-701-719-6971 don suraren (Tashar Ƴanci 103.1 FM Kaduna) kai tsaye ta wayar hannu. Musamman Ga Waɗanda Suke Ƙasar Amurka.

Kuna iya turo mana labari ko shawara a: info@libertytvradio.com

Leave a Reply