Home Labaru Fansho: Shugaba Buhari Ya Shirya Biyan Tsofaffin Ma’aikata Hakkokin Su

Fansho: Shugaba Buhari Ya Shirya Biyan Tsofaffin Ma’aikata Hakkokin Su

536
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya fara shirye-shiryen kawo karshen jinkirin biyan makudan kudaden da gwamnati ke biyan ‘yan fansho.

Buhari ya umarci ministar kudi da kasafida tsare tsare Zainab Ahmed ta gyara, tare da sakin naira biliyan 62 da miliyan 83 domin fidda hakkokin ‘yan fansho.

shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari

A cikin wata wasika da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari yasanya wa hannu, an umarci ofishin kasafi ya hada naira biliyan 12 da miliyan 83 na shekara ta 2020, da naira biliyan 25 ta shekara ta 2021, da kuma naira biliyan 25 na shekara ta 2022 domin biyan fansho ga ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Shugaba Buhari, ya kara da umartar ministar kudi ta tabbatar da sakin kudin gabadaya bayan hukumomin da yakamata sun amince.