Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Nijeriya, ta ce ta
dakatar da ayyukan jirgin sama na Max Air ƙirar Boeing 737
nan take.
Da ta ke bayyana dakatarwar a cikin wata sanarwa da Daraktan kula da Ayyuka da Horarwa da kuma bada Lasisi na hukuamr Kyaftin Ibrahim Dambazau da Babban Daraktan ta Kyaftin Musa Nuhu su ka fitar, hukumar ta ce ta dauki matakin ne saboda wasu al’amurra da su ka faru da jiragen kamfanin.
Daga cikin abubuwan hukumar ta lissafa kuwa akwai lalacewar Wilin tayar saukar jirgi ta gaba, wadda ta janyo wani mummunan lamari ga jirgin tsakanin tashin sa daga filin jirgin sama a jihar Adamawa zuwa saukar sa a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Hukumar, ta kuma sake soke tashin jirgin ne a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano, saboda fitar iskar gas mai tsananin zafin a jirgin a ranar 11 ga watan Yuli na shekara ta 2023.
Haka kuma, hukumar ta ce ta kafa wata tawagar jami’an bincike da za su bi diddigi game da harkokin kamfanin, kuma dole sai sun gamsu da sakamakon binciken kafin ta ba jirgin damar ci-gaba da ayyukan sa.