Home Labaru Kotu Ta Baiwa Hukumar DSS Wa’Adin Mako Guda Don Sakin Godwin Emefile

Kotu Ta Baiwa Hukumar DSS Wa’Adin Mako Guda Don Sakin Godwin Emefile

76
0

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ba hukumar tsaro ta
farin DSS wa’adin mako guda ta gurfanar da tsohon gwamnan
babban bankin Nijeriya Godwin Emefile ko kuma ta sallame
shi.

A farkon watan da ya gaba ta ne gwamnatin tarayya ta dakatar da Godwin Emefile, sannan bayan kwanaki biyu hukumar DSS ta sanar da kama shi a daidai lokacin da ya ke yunkurin ficewa daga Nijeriya.

Emefile dai ya maka hukumar DSS kara ne a karkashin lauyan sa J.B Daudu, yana mai bukatar kotun ta tilasta wa hukumar DSS ta sake shi.

Lauyan, ya kuma roki kotun ta ayyana duk zarge-zargen da ake yi wa Emefile da kuma tsare shi da ake ci-gaba da yi a matsayin take masa hakki.

J.B Daudu, ya kuma cigaba da rokon kotun ta tilasta wa hukumar DSS biyan wanda ya ke karewa diyyar Naira Biliyan biyar, saboda bata ma shi lokaci da kuma tsare shi ba bisa ka’ida ba.

Leave a Reply