Home Labaru Amnesty International Ta Nada Isa Sanusi Sabon Shugaban Ofishinta A Najeriya

Amnesty International Ta Nada Isa Sanusi Sabon Shugaban Ofishinta A Najeriya

256
0

Ƙungiyar kare hakkin Bil-Adama ta Amnesty International, ta
sanar da naɗin mai fafutukar kare haƙƙin dan-Adam kuma
tsohon dan jarida Isah Sanusi a matsayin sabon daraktan ta a
Nijeriya.

Wata sanarwa da shugaban kwamitin amintattu na Amnesty a Nijeriya Auwal Musa Rafsanjani ya fitar, ta ce Isah Sanusi zai jagoranci fadada ayyukan bincike da gangamin kungiyar a Nijeriya.

Haka kuma, zai maida hankali a kan al’amuran da su ka shafi rikice-rikice da ilmi da kare hakkin dan-Adam da daidaiton jinsi da sauyin yanayi da shigar da matasa cikin harkokin ingantawa da kare hakkin Bil-Adama.

Auwal Musa Rafsanjani, ya ce Isa Sanusi dai ya na da gogewar aiki ta tsawon shekaru bakwai, lamarin da ke nufin zai bada gudummawa wajen ci-gaba da ganin tasirin ayyukan Amnesty a Nijeriya.

Kafin sabon nadin sa dai, Isah Sanusi shi ne shugaban yaɗa labarai da sadarwa na Amnesty a Najeriya, mukamin da ya ke rike da shi tun a shekara ta 2016, sannan ya taɓa aikin jarida da kafar BBC tsawon shekaru 10, kuma ya taɓa rike mukamin
mataimakin editan jaridar Daily Trust.

Leave a Reply