Home Labarai Nan Da Karshen Shekara Za Mu Kammala Aikin Gidan Yarin Kano, Abuja...

Nan Da Karshen Shekara Za Mu Kammala Aikin Gidan Yarin Kano, Abuja Da Ribas – Aregbesola

354
0

Ministan Harkokin Cikin Gida Rauf Aregbesola, ya ce gwamnatin tarayya za ta kammala ginin gidajen yari uku, wadanda kowannen su zai dauki fursinoni dubu 3 nan da watan Disamba na shekara ta 2022.

Gidajen yarin kuwa sun hada da na jihohin Kano da Rivers da kuma birnin tarayya Abuja.

Aregbesola ya bayyana wa ma nema labarai haka ne, bayan wani rangadi da ya kai gidan yarin da ke Karshi a birnin Abuja inda ya ce an kusa kammala wanda ke Kano yayin da aka kammala kashi 55 cikin 100 na aikin gidajen yarin jihar Rivers da birnin Abuja.

Ministan ya kara da cewa, burin shi kawai shi ne a samu guda uku na farko daga cikin ayyuka shida da za a kammala kafin wa’adin wannan gwamnatin ya kare.

Ya ce su na da irin wannan aikin a Kano kuma ya kusa kammaluwa. ya na mai cewa ya yi imanin kafin watan Disamba shugaban kasa ne zai kaddamar da shi.

Leave a Reply