Home Labarai Kotu Ta Ba Hukumar DSS Ikon Ci-gaba Da Rike Tukur Mamu

Kotu Ta Ba Hukumar DSS Ikon Ci-gaba Da Rike Tukur Mamu

142
0

Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta ba hukumar tsaro ta farin kaya DSS izinin ci-gaba da tsare Tukur Mamu na tsawon watanni biyu.

A ranar 12 ga watan Satumba dai, Hukumar DSS ta bukaci kotu ta ba ta damar kammala binciken ta a kan Tukur Mamu.

A karar dai, lauyan DSS Ahmed Magaji ya bukaci karin kwanaki 60.

A hukuncin da yanke, mai shari’a Nkeonye Maha ya ba hukumar DSS damar ci-gaba da tsare shi Tukur Mamu.

Leave a Reply