‘Yan banga sun yi nasarar fille kan wani gawurtaccen dan bindiga tare da kama wasu shida da ran su a Jihar Katsina.
Wata majiya ta ce, ‘yan bindigar sun kwashi kashin su a hannun ‘yan bangar ne, a wani hari da ‘yan bindigar su ka kai a Karamar Hukumar Batsari, inda wasu majiyoyin su ka tabbatar da cewa an kama ‘yan bindiga akalla shida.
Majiyoyin sun ce ‘yan bindiga tara aka kashe, amma wani bidiyo da ka yada bayan artabun ya nuna wata gawa da aka file wa kai tare da sare kafar ta guda.
Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, ‘yan bindigar sun kai harin garin ne da misalin karfe 4:30 na yammacin ranar Lahadin da ta gabata, inda su ka kashe mutum daya su ka kuma samu wani da harbi.
Yayin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Katsina SP Gambo Isah, ya ce bai samu rahoto daga DPO na yankin ba, sai dai yay i alkawarin cewa zai tuntubi ‘yan jarida idan ya samu bayani.














































