Home Home Najeriya Za Ta Kaddamar Da Kofofi Masu Amfani Da Na’ura A Tashoshin...

Najeriya Za Ta Kaddamar Da Kofofi Masu Amfani Da Na’ura A Tashoshin Jiragen Saman Kasar A Watan Maris

122
0

A kokarinta na saukakawa matafiya zirga-zirga a filayen tashi da saukar jiragen kasa, gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na kaddamar da kofofi masu amfani da na’urar lantarki a filin saukar jiragen saman kasa da kasa a Najeriya a watan Maris me kamawa.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayyana hakan a Abuja jim kadan bayan kammala rangadin duba kayayyakin aiki a tashar jiragen saman, yace yanzu za’a samu sauki wajen daukar hoton takardun tafiye-tafiye idan aka kaddamar da kafofin masu amfani da na’ura a filayen saukar jiragen saman.

Ministan ya kuma gudanar da rangadi a cibiyar da ayyukan hukumar kula da shige da ficen Najeriya sa’annan ya baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewar kammala ginin cibiyar zai inganta yanayin tsaro a Najeriya.

A cewar Tunji-Ojo, samun yawaitar kofofin masu amfani da na’ura, zai saukaka zirga-zirgar fasinjoji a tashoshin jiragen saman kasar.

Leave a Reply