Home Home Majalisar Dinkin Duniya Ta Kakaba Wa ‘Yan Tawayen Jamhuriyar Congo Takunkumai

Majalisar Dinkin Duniya Ta Kakaba Wa ‘Yan Tawayen Jamhuriyar Congo Takunkumai

31
0

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kakaba takunkumai a kan jagororin kungiyoyin ‘yan tawaye 6 da ke fada a sassan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, a yayin da ake ci gaba da gwabza yaki a arewa maso gabashin kasar mai fama da rikici.

Kwamitin ya antaya takunkuman hana sayen makamai da na tafiye-tafiye a kan manyan jami’an kungiyar ‘yan tawayen Allied Democratic Forces ADF biyu, da kuma wani jagora a cikin kungiyar ‘yan tsagera ta Twirwaneho, da kuma wani guda daga kungiyar ‘yan tawayen National Coalition of the People for the Sovereignty of Congo.

A wata sanarwa, mataimakin wakilin Amurka na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Robert Wood ya bayyana farin cikinsa da matakin kwamitin takunkumai a kan jagororin kungiyoyin ‘yan tawaye 6 a Congo, inda ya ce wadannan mutane ne ke da alhakin dimbim ayyukan cin zarafi a kasar.

Leave a Reply