Home Home Bankin Raya Kasashen Afirka Ya Yi Gargadin Cewa Hauhawar Farashin Kayayyaki Na...

Bankin Raya Kasashen Afirka Ya Yi Gargadin Cewa Hauhawar Farashin Kayayyaki Na Iya Haifar Da Tarzoma A Tsakanin Al’umma

34
0

Bankin raya kasashen Afirka ya yi gargadin cewa hauhawar farashin makamashi, abinci da sauran kayayyaki a wasu kasashen Afirka ciki harda Najeriya, na iya haifar da tarzoma a tsakanin al’umma.

Sanarwar Bankin na kunshe ne a cikin wani rahoto da aka fidda a makon jiya.

Bankin ya ce a hasashensa na shekarar 2024, karuwar farashin makamashi da abinci, tare da faduwar darajar kudin kasashen Angola, Habasha, Kenya da Najeriya, na iya haifar da rikicin cikin gida, duk da cewa nahiyar Afirka na nuna alamun samun ci gaban tattalin arziki.

Bankin ya kuma ce tashin hankali a gabashin Turai da Gabas ta Tsakiya na iya haifar da kalubale wajen samar da kayayyaki, da kara hauhawar farashin kayayyaki a fadin duniya, lamarin da zai sa yanayin ya dada muni a Afirka.

Tuni aka fara zanga-zanga a wasu sassan Najeriya saboda yadda yunwa da tsadar rayuwa ke karuwa a Najeriya.

Leave a Reply