Home Home Mutuwar Dalibi: ‘Yan Sanda A Legas Na Bincike

Mutuwar Dalibi: ‘Yan Sanda A Legas Na Bincike

63
0
Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike kan mutuwar marigayi Sylvester Oromoni, mai shekara 11 dalibin kwalejin Dowen da ake zargin wasu dalibai da cin zarafin sa wanda ya kais hi har lahira.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Hakeem Olusegun Odumosu ya bayyana cewa an umurci sashin kisan kai na sashen binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar legas wato SCID dake Panti, da ya karbe shari’ar daga sashin Maroko.

Kwamishina Odumosu, ya kara da cewa rundunar na hada kai da rundunar ‘yan sandan jihar Delta wajen gudanar da bincike domin bankado sirrin da ke tattare da mutuwar karamin yaro Sylvester Oromoni wanda ake zargin daliban ajin karshe na makarantar sakandare suka yi ajalin sa ta hangar lakada masa duka, da kuma ba shi wani sindarin chemical da ba’a iya tantancewa ba.

Marigayi dalibin wanda saura yan kwanaki ya cıka shekaru 12 a duniya ya mutu ne a ranar Talata, bayan da ya sami raunuka da dama bayan zargin da ake yi cewa wasu manyan daliban makarantar sun gana masa azabar duka da cin zarafi mai tsananin gaske a yayin da yake dakin bacci da wasu dalibai.