Home Home Cancantar Tsayawar Atiku Takara: Kotu Ta Sa Ranar Yanke Hukunci

Cancantar Tsayawar Atiku Takara: Kotu Ta Sa Ranar Yanke Hukunci

95
0
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 21 ga watan Fabrairun 2022 domin yanke hukunci kan ko tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya cancanci tsayawa takarar Shugaban Kasa a babban zaben 2023.

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 21 ga watan Fabrairun 2022 domin yanke hukunci kan ko tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya cancanci tsayawa takarar Shugaban Kasa a babban zaben 2023.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Inyang Ekwo ne ya sanya ranar, bayan kammala sauraron muhawara tsakanin lauyoyin bangarorin biyu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya rawaito wani kamfani mai zaman kansa mai suna EMA ne ya maka Atikun da jam’iyyar PDP da hukumar zabe INEC da kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya a gaban kotun.

Kamfanin dai na kalubalantar cancantar Atikun ta tsayawa takarar Shugaban Kasa, bisa hujjar cewa ba asalin dan Najeriya ba ne ta nasabar haihuwa inda ya roki kotun ta yi la’akari da tande-tanaden sashe na 25(1) da (2) da kuma 131(a)na Kundin Tsarin Mulki wajen hana shi takarar.

A baya dai Gwamnatin Jihar Adamawa ta roki kotun da ta saka ta cikin wadanda ake tafka shari’ar da su, inda a ranar 27 ga watan Yulin 2021 kotun ta amince da hakan.

Jihar dai ta shaida wa kotun cewa Atikun ya cancanci tsayawa takara, kuma har ya taba jagorantar Jihar da kuma zama Mataimakin Shugaban Kasa na tsawon shekara takwas.

To sai dai lauyan masu kara, Oladimeji ya ce ko da yake a Najeriya aka haifi Atiku, hakan ba yana nufin shi dan Najeriya ba ne, a cewarsa, kasancewar an yi kuskure a baya, ba ya nufin a sake maimaita hakan a yanzu.