Home Labarai Zaben Gambia: Adama Barrow Ya Yi Nasara A Karo Na Biyu

Zaben Gambia: Adama Barrow Ya Yi Nasara A Karo Na Biyu

215
0

Hukumar zabe mai zaman kanta a Gambia ta sanar da Shugaba Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka gudanar a ranar Asabar.

Alkaluman da hukumar zaben kasar Gambia ta fitar ya nuna cewa, Mista Barrow ya samu kuri’u kusan sau biyu fiye da wanda babban abokin hamayyar sa Ousainou Darboe ya samu wato kashi 53  da kashi 28.

Adamu Baro ya lashe kuri’u dubu 457 da 519 yayin da dan takarar jam’iyyar adawa Ousainou Darbor ya samu kuri’u dubu 238 da 253.

Tun farko sakamako daga gundumomi hamsin daga cikin gundumomin 53 na kasar sun ba shugaba Barrow damar jagoranci.

Sai dai babban mai kalubalantar sa, Ousainou Darboe, da wasu ‘yan takara biyu sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka nuna rashin amincewa da alkaluman.

Ousainou Darboe, da wasu ‘yan takara biyu sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka nuna rashin amincewa da alkaluman.

Leave a Reply