Home Labaru Mutum 4 Sun Kamu Da Coronavirus a Kano

Mutum 4 Sun Kamu Da Coronavirus a Kano

364
0
Mutum 4 ke nan suka kamu da cutar a fadin jihar Kano, kawo yanzu
Mutum 4 ke nan suka kamu da cutar a coronavirus a jihar Kano, kawo yanzu

Yawan mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Jihar Kano ya sake karuwa a ranar Talata.

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta tabbatar da kamuwar mutum na 4 da cutar a jihar, bayan fitowar sakamakon gwajin da aka yi masa.

Gwamnatin jihar ta ce mutum na 4 da ya kamu da cutar ya samu kusanci da wanda ya fara harbuwa da cutar a jihar Kano.