Home Labaru Kano: An Hana Fita Saboda Coronavirus

Kano: An Hana Fita Saboda Coronavirus

694
0
An ba wa jami'an tsaro umurnin tabbatar da ganin jama'a sun bi dokar hana fitar a fadin jihar.
Dokar hana zirga-zirgar za ta fara aiki daga ranar Alhamis har na tsawon kwana bakwai a karon farko.

Gwamntin Jihar Kano ta sanya dokar hana fita a fadin jihar da zummar dakile yaduwar cutar coronavirus a jihar.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya sanar da haka yayin ganawarsa da ya yi da malaman addini a ranar Talata.

Dokar hana fitar ta tsawon kwana bakwai a matakin farko, za ta fara aiki ne daga ranar Alhamis 16 ga watan Afrilun da muke ciki.

Sanarwar da kakakin gwamnan, wato Salihu Tanko Yakasai ya fitar ta ce gwamantin jihar ta umurci jami’an tsaro su tabbatar an bi dokar hana zirga-zirgar yadda ya kamata a fadin jihar.