Home Labaru Masu Coronavirus Sun Kai 362

Masu Coronavirus Sun Kai 362

469
0

Masu cutar coronavirus sun karu da mutum 19, zuwa 362 a Najeriya.

Cibiyar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya NCDC ta ce adadin masu ya karu ne bayan karin mutum 19 sun harbu da cutar a ranar 14 g watan Afrilun 2020.

Sabbin wadanda suka kamu da cutar suna hada da mutum 14 a Jihar Legas da kuma mutum 2 a Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Sauran sun hada da karin mutum daya-daya a jihohin Kano, Akwa-Ibom da kuma Edo.

Ya zuwa yanzu an sallami mutum 99 daga asibiti bayan sun wake daga cutar.

Sai dai kuma cutar ta coronavirus ta yi sanadiyar mutuwar mutum 11 daga cikin mutum 362 da suka kamu da ita tun farkon bullar cutar a Najeriya.

Hakan ke nufin zuwa yanzu masu cutar 252 ne ke killace a asibiti.