Home Coronavirus Mutum 3 Sun Warke Daga COVID-19 A Bauchi

Mutum 3 Sun Warke Daga COVID-19 A Bauchi

751
0
Bala Mohammed ne na farko da COVID19 ta kama a jihar Bauchi.
An sallami mutum 3 da suka warke daga cutar coronavirus a jihar Bauchi

An sallami masu cutar coronavirus 3 bayan sun warke daga cutar a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya.

Gwajin karshen da aka yi wa mutanen a cibiyar killace masu dauke da cutar coronavirus a jihar Bauchi ya tabbtar da cewa yanzu ba sa dauke da kwayar cutar.

Gwamnan Jihar Bala Mohammed ya bayyana farin cikinsa game da sallamar wadanda suka warken ta shafinsa na twitter.

Da yake bayyana godiyarsa ga Allah game da nasarar da aka samu, Bala Mohammed ya kuma shawarci mutane da su rika bayar da tazara a tsakanincsu tare da kula da matakan kariya da na tsafta.

Bala Mohammed ne na farko da COVID19 ta kama a jihar Bauchi.

Gwamnan wanda shi ne mutum na farako da ya kamu da cutar a jihar, amma daga bisani ya warke, ya kuma jinjina wa ma’aikatan lafiya bisa jan aikin da suke yi na yaki da annobar ta COVID-19.