Home Labaru Hajjin 2020: Akwai Yiwuwar Gudanar Da Aikin Hajji NAHCON

Hajjin 2020: Akwai Yiwuwar Gudanar Da Aikin Hajji NAHCON

345
0
Hajjin 2020: Akwai Yiwuwar Gudanar Da Aikin Hajji NAHCON

Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta ce akwai yuwuwar a gudanar da aikin hajji a wannan shekara ta 2020.

Shugaban hukumar Zikrullah Kunle Hassan ya sanar da haka a wata zantawa da gidan rediyon tarayya ya yi dashi.

Kunle Hassan ya ce alamu daga ma’aikatar lafiya ta kasar Saudiyya na nuna ana samu raguwar barkewar annobar Coronavirus, wanda hakan alamace ta za a yi aikin hajji a wannan shekarar.

Bisa haka ne Zikrullah Kunle Hassan ya shawarci maniyyata su fara biyan kudin aikin hajjin koda da kadan-kadan ne don akwai yuwuwar a yi aikin hajji, amma za a rage yawan mutane saboda annobar COVID-19.

Zikrullah ya kuma bukaci daukaci Musulman Nijeriya da ke da niyyar yin aikin hajjin su yi addu’a tare da amfani da duk wasu matakan da suka dace.

Shugaban hukumar NAHCON ya kara da cewa, duk da hangen hukumar na yuwuwar yin aikin hajjin bana, ta dakatar da shirin ta, sai dai ya tabbatar da cewa, hukumar ba za ta samu wata asara ta kudi ba,sakamakon ta na gudanar da ayyukan ta ne a shari’ance.