Home Coronavirus Coronavirus: Mutum 3 Sun Kara Mutuwa A Legas

Coronavirus: Mutum 3 Sun Kara Mutuwa A Legas

386
0
Gwamna Babajide Sanwo-Olu (a tsakiya) a lokacin bude wurin killace masu cutar coronavirus a jihar Legas.
Karon farko ke nan da annobar coronavirus ta yi sanadiyyar mutuwar likita a jihar Legas.

Annobar COVID19 ta kashe karin mutum 3 a Legas, lamarin da ya kai yawan mutanen da cutar ta kashe a jihar zuwa 10.

Cikin mamatan da cutar ta kuma kashe har likita na farko da ta yi ajalinsa a jihar, sakamakon mu’amala da ya yi da wani mai cutar da ya dawo daga kasashen ketare.

Kwamishinan Lafiyan jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ya ce karin mamatan maza ne masu shekaru 51, 52 da kuma 62.

A sakon da ya wallafa a shafinsa, Farfesa Abayomi ya bukaci jama’ar jihar da su rika lura tare da kai rahoton bullar cutar ga hukumomin da ke yaki da annobar.

A Jihar Legas ce aka fara samun bullar cutar COVID19 a Najeriya, kuma kawo yanzu jihar ce ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar a fadin kasar.