Home Labaru Mun San Ranar Da Za A Daina Sata Da Garkuwa Da Mutane...

Mun San Ranar Da Za A Daina Sata Da Garkuwa Da Mutane A Nijeriya – NFIU

70
0

Shugaban hukumar leken asirin kudade ta kasa Modibbo Tukur, ya ce nan da zuwa watan Afrilu na shekara ta 2022 za a daina sata da kuma yin garkuwa da mutane a Nijeriya.

Hukumar dai wani sashe ne na Babban bankin Nijeriya CBN, wanda ke bibiyar masu daukar nauyin ‘yan ta’adda, da kuma yaki da barayi masu safarar kudaden Nijeriya kasashen ketare.

Moddibo ya bayyana haka ne, a wani taron kara wa juna sani, wanda aka shirya a kan yaki da safarar kudade da kuma daukar nauyin ta’addanci a Abuja, inda ya ce ranar karshe ta ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane tsakanin watannin Maris da Afrilu na shekara ta 2022 ne.

Ya ce sun yi hasashen ne sakamakon wani bincike da ma’aikatar ta gudanar, kuma irin wannan hasashen ne aka yi domin ganin karshen ‘yan ta’addan Boko Haram.

Moddibo, ya ce ranar 15 ga watan Satumba na shekara ta 2021 aka yi hasashen ita ce karshen Boko Haram a Nijeriya, kuma haka ta cimma wannan, sakamakon toshe hanyoyin da yan ta’addan ke samun kudi.