Home Home Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kwace Iko Da Zauren Majalisar Dokoki Ta Jihar...

Jami’an ‘Yan Sanda Sun Kwace Iko Da Zauren Majalisar Dokoki Ta Jihar Filato

66
0

Hukumar ‘yan sanda ta ƙwace iko da zauren majalisar dokoki ta jihar Filato, sannan ta hana kowane ɓangare daga cikin shugabannin majalisar shiga zauren majalisar.

Lamarin dai, ya biyo bayan rikicin da ya barke a majalisar ne game da wanene halastaccen shugaban ta, bayan an tsige Yakubu Sanda mai wakiltar mazaɓar Pengana ta ƙaramar hukumar Bassa.

Wata majiyar ‘yan sandan ta shaida wa manema labarai cewa, mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya mai kula da shiyyar jihohin Filato da Benue da Nasarawa Mustapha Dandaura ne ya bada umarni.

Bayan ziyarar da ya kai birnin Jos domin gane wa idon sa halin da ake ciki a kan Lamarin, Mustapha Dandaura ya bada umarnin a kwace zauren majalisar baki ɗaya, a wani mataki na kauce wa abin da ka iya zuwa ya dawo na karya doka.