Home Labaru Jam’iyyar APC Ta Na Fama Da Rigingimu A Jihohi 13

Jam’iyyar APC Ta Na Fama Da Rigingimu A Jihohi 13

19
0

Rahotanni na cewa, har yanzu Jam’iyyar APC ba ta gama cimma matsaya game da ranar da za ta shirya zaben shugabannin ta na kasa ba.

Tun farko dai an tsaida watan Yuni na shkara ta 2021, amma daga bisani aka sake kara wa su Mai Mala Buni wa’adin watanni shida.

Wasu daga cikin abubuwan da su ka janyo tsaiko a kan tsaida lokacin babban taron na kasa, sun hada da rashin yi wa ‘yan jam’iyyar rajista a jihohin Zamfara da Anambra, baya ga matsalolin da su ka biyo bayan zaben shugabanni da aka gudanar a jihohi da kananan hukumomi da kuma mazabu.

Yanzu haka akwai jihohi akalla 13 da rigingi mu su ka barke bayan an shirya zaben shugabannin jam’iyyar, inda ‘yan ta-ware su ka sha alwashin ba za su janye karar da su ka shigar kotu ba.